Kotu a Ghana ta yanke wa wasu mutane hudu da suka hada da dan sanda da wani soja hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari saboda samun su da laifin jagorantar wata kungiyar ‘yan aware ba bisa ka’ida ba.
Wallafawa ranar:
Minti 2
Ana zargin kungiyar ‘yan awaren Western Togoland Restoration Front (WTRF) da kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda tare da toshe hanyoyin da ke kusa da kan iyaka da Togo a shekarar 2020, a wani mataki na neman ‘yancin kai na wani yanki mai suna Western Togoland.
« Wannan hukuncin ya zama gargadi mai karfi game da duk wani yunkuri na yin barazana ga zaman lafiyar kasar Ghana , » in ji mai shari’a Mary Maame Ekueh Yanzuh yayin yanke hukunci a Accra, babban birnin Ghana.
Wanda ya kafa kungiyar Michael Koku Kwabla zai share tsawon shekaru biyar da tarar dalar Amurka 940 (kusan Yuro 860) a gidan yari, yayin da sauran mambobin kungiyar Nene Kwaku da Emmanuel Afedo da Abednego Mawena aka yanke musu hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari kowannen su.
A shekara ta 2017, aka kama shugabannin ‘yan aware a yammacin Togoland tare da hana su duk wani yukunri gudanar da ayukan su .
Yankin kogin Volta yana da kabilu da yawa kuma tarihinsa na baya-bayan nan ya samo asali ne daga turawan mulkin mallaka guda uku.
Birtania ta mamaye mafi yawan abin da ya kunshi Ghana da Jamus da ke rike da kasar Togo a yanzu.
Bayan yakin duniya na farko da kuma shan kashi da Jamus ta yi, Birtania da Faransa sun raba kayan Jamusawa a tsakaninsu. Faransa ta dauki Togo a yau.
Biritania ta kwace Togoland na Biritaniya, yankin da aka hade cikin Ghana a 1956 bayan faduwar daular a Afirka.
‘Yan awaren dai sun ce yankin na da nasa tarihi da al’adu kuma suna son mayar da yankin ya zama kasa mai cin gashin kanta
Crédit: Lien source
Les commentaires sont fermés.