Adadin waɗanda suka kamu da cutar Ebola ya ƙaru sama da 200 a Congo da Uganda

An samu ƙaruwar mutane da suka kamu da kwayar cutar Ebola, sama da mutane 200 suka harbu da cutar, kusan wata guda bayan bullar ta, sanarwar da ke zuwa wani lokaci da taron ƙasashe ya samar da kudade ga Uganda da DR Congo.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Sanarwar da ke zuwa yan lokuta bayan kamala taron shugabanin ƙasashe, inda shugaban hukumar zartarwa ta AU, Évariste Ndayishimiye kuma  Shugaban Burundi ya sanar da kudaden da aka tattara da yakai kusan Dala milyan 910, wanda ƙasashen Afrika suka samar da kusan milyan 80 daga cikin su ga ƙasashen na Uganda da DR Congo za su amfana da su a yakin da suke yi da wannan cuta.

Alkaluman da ake da su na bayyana cewa kusan mutane 875 suka harbu da  cutar, inda mutane 202 a DR Congo suka rasa rayukansu tun bayan barkewar ta a ranar 15 ga watan Mayu,19 da kuma wau da suka kamu a Uganda, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.

Samar da wannan talafi na kudi a cewar shugaban sashen gaggawa na cibiyar yaki da cuttuka ta Africa CDC, Wessam Mankoula, shirin ya ƙunshi daukar matakan  yaki da cutar nan take a yankunan da abin ya shafa,wato DRCongo da Uganda.

Mahmoud Ali Youssouf, Shugaban hukumar tarayyar Afirka ya bayyana kwarin gwiwar da suke da ita,tare da yin kira na ganin jam’a sun yi amfani da gargadi daga jami’an kiwon lafiya,baya ga yin kira ga hukumomin ƙasashe na ganin sun yi amfani da wanan tallafi ta hayar da ta dace.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.