Ana zargin sojojin Najeriya da ƴan banga da kashe fararren hula kan iyaka da Benin

Ana zargin daya daga cikin kungiyoyi ƴan banga masu dauke da makamai da ke aiki karkashin inuwar sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar dakarun jamhuriyar Benin da kashe makiya Fulani da dama da ake zargi da kasancewa masu tseguntawa mayaka masu ikirarin jihadi ta Ansaru da labarai, a wani hari da suka kai gundumar Bussa da ke maƙwabciyarta a sansanonin makiyaya Fulani da ke kewaye da Kabe a tsakiyar Najeriya a ranar Alhamis.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

 

Rahotanni daga yankin na bayyana cewa harin ya faru ne a Jihar Naija, a tsakiyar Najeriya,inda wasu daga cikin mayakan na Ansaru ke amfani da shi wajen kai hare-hare.

Tun a shekara ta 2021,bayan rarrabuwar ƙungiyar boko haram,wani bangare daga cikin mayakan suka samar da ƙungiyar Ansaru karkashin inuwar ƙungiyar Al-Qaeda a yankin Maghreb (AQIM).

Rahotanni da ke karo da juna na tabbata da cewa,ƴan banga daga Najeriya musamman daga gundumar Bussa da ke maƙwabciyarta sun kai hari kan sansanonin makiyaya na Fulani da ke kewaye da Kabe, a gundumar Borgu na Jamhuriyar Benin.

An kuma bayyana cewa sun kama matasa da dama da ake zargi da kasancewa masu taimakawa Ansaru da rahotanni ,baya ga haka  suka kuma kashe waɗanda suka nemi bijere musu.

Akala sun « kashe mutane 41 da ake zargi da taimakawa Ansaru a lokacin hare-haren, inda aka kama wasu da yawa, » in ji Ahmad Ali, wani shugaban al’umma daga ƙauyen Konkoso da ke kusa.

Rahotanni na bayyana cewa « harin haɗin gwiwa ne tsakanin ‘yan banga da waɗanda suka fito daga maƙwabciyar Benin, tare da taimakon sojojin Najeriya, » in ji Ahmad Ali.

Ya zuwa wannan lokaci ,kakakin rundunar sojin Najeriya ya kaucewa bayar da karin haske a kan wannan al’amari da ya faru a kauyen Kabe, a gundumar Borgu,kazalika bangaren jamhuriyar Benin sun kaucewa bayar da ƙarin bayani a kai.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.