Cape Verde ta sake doke Mozambique da kwallaye 3 bayan nasara kan Ghana

Cape Verde ta yi nasara da kwallaye 3 da nema akan Mozambique a wasansu na yau Juma’a karkashin gasar cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana a Ivory Coast.

Wallafawa ranar:

Minti 1

Wannan nasara ta bai wa kasar damar ci gaba da da zama jagorar rukuninta na B da maki 6 bayan nasara a dukkanin wasanninta biyu.

A karawarta ta farko, Cape Verde ta doke Ghana ne da kwallaye 2 da 1, inda a yanzu ta ke matsayin tawaga mafi samun nasara a rukuninta.

Nasarar ta Cape Verde ta sanya sauran kasashen rukunin 3 da suka kunshi Masar da ke matsayin ta 2 da maki 2 kana Ghana a matsayin ta 3 da maki 1 haka zalika Mozambique da maki 1 a tsaka mai wuya.

A wasan farko dai Masar ta yi canjaras da Mozambique ne da kwallaye 2 da 2 haka zalika da Ghana wanda ke nuna ta na bukatar gagarumar nasara a wasanta na ranar Litinin da za ta hadu da Cape Verde, tawagar da har zuwa yanzu ba ta yi rashin nasara a gasar ba.

Duk dai a rana guda ne itama Ghana za ta kara da Mozambique, wanda zai bayan wasanni biyun ne za a tabbatar da wadanda za su tsallaka mataki na gaba da kuma wadanda za su fice daga gasar.

Rukunin na B dai na sahun rukunnai mafiya tarnaki a gasar ta AFCON wadda kasashe 24 ke fafatawa don lashe kofin da yanzu haka ke hannun Senegal.

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.