A Burkina Faso, hukumomin riƙon ƙwarya sun gabatar da rahoton ci gaba kan ayyukan sake ƙwato yankunan ƙasar a jiya Juma’a. Sanarwar da ministan yaƙi da tsaron ƙasa ya tabbatar inda ya fitar da wasu alkaluma na cewa Burkina Faso yanzu tana iko da kusan kashi uku cikin huɗu na ƙasar wanda ake iya kwantantawa da kashi 74.53%.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Ministan yaƙi da tsaron ƙasa na Burkina Faso, Janar Célestin Simporé, ya karasa da cewa fararen hula da hukumomin gwamnati sun koma waɗannan sabbin yankunan da aka kwato daga hannun ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
A karshe ministan ya na mai cewa, « Za mu iya zuwa ko’ina, kuma za mu je can, » domin ci gaba da ayyukan ci gaban ƙasa da kuma samarwa jama’a ababen more rayyuwa.
Janar din ya kuma yi nuni da kokarin da aka yi a cikin ‘ƴan watannin nan dangane da kayan aiki, ga sojojin da ke yaƙi da ƴan ta’adda.
Harkoki na ci gaba da gudana a yankuna da dama na ƙasar ta Burkina Faso.
Sanarwar ministan na zuwa ne yayin da ƙungiyoyin ‘ƴan ta’adda masu dauke da makamai ke ƙara sa kai zuwa wasu yankunan ƙasar ta Burkina Faso.
A ranar Talata farkon wannan mako, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kuma sun kwace iko da rundunar sojoji a Tawori, a lardin Tapoa, wanda suka kwace, a cewar majiyoyi da dama a yankin Gabas.
Washegari, a yankin Kudu maso Yamma, wasu sansanonin ‘yan ta’adda da dama mallakar ‘ƴan sa-kai don Tsaron Gida sun fuskanci hari daga mayakan ‘yan ta’adda.
Crédit: Lien source