Gwamnatin Ghana ta amince da shawarar ƙara wa’adin mulkin shugaban ƙasa daga shekaru huɗu zuwa biyar, tare da rage yawan shekarun da sai mutum ya kai zai iya tsayawa takarar jagorancin ƙasar zuwa 35.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
A shekarar da ta gabata ne shugaba John Dramani Mahama ya kafa kwamiti da zai yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1992 garambawul, inda ya gabatar da shawarwarinsa ga gwamnatin.
Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a na Ghana, Dominic Ayine, ya ce baya ga ƙara wa’adin shugaban ƙasar, za a ƙara na ƴan majalisa ma domin ya yi dai-dai da sabon tsarin shugabancin.
Ayine ya ce watannin farko na kowace gwamnati na zama na ƙoƙarin karbar ragama daga tsoffin shugabannin, yayin da lamarun zaɓe ke mamaye watannin ƙarshe, a don haka ƙara shekarun zai bai wa gwamnatocin ƙarin damar gudanar da ayyuka.
Gwamnatin Ghana ta amince da shawarar da kwamitin ya bayar na rage shekarun da ɗan takarar shugaban ƙasa ya kamata ya cika kafin neman mulki, daga 40 zuwa 35, maimakon 30 da kwamitin gyara dokokin ƙasar ya bayar.
Ƙudirin dokar ƙara wa’adin mulkin shugaban ƙasar sai ya tsallake wasu matakai gabanin gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a a shekarar 2027, kuma dole ne aƙalla kashi 75 cikin 100 na masu zaɓe su kaɗa ƙuri’ar amincewa dashi kafin zama doka.
Crédit: Lien source