Kotu a Ghana ta zartas da hukuncin daurin shekaru biyar ga ‘yan aware

Kotu a Ghana ta yanke wa wasu mutane hudu da suka hada da dan sanda da wani soja hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari saboda samun su da laifin jagorantar wata kungiyar ‘yan aware ba bisa ka’ida ba.

Wallafawa ranar:

Minti 2

Ana zargin kungiyar ‘yan awaren Western Togoland Restoration Front (WTRF) da kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda tare da toshe hanyoyin da ke kusa da kan iyaka da Togo a shekarar 2020, a wani mataki na neman ‘yancin kai na wani yanki mai suna Western Togoland.

« Wannan hukuncin ya zama gargadi mai karfi game da duk wani yunkuri na yin barazana ga zaman lafiyar kasar Ghana , » in ji mai shari’a Mary Maame Ekueh Yanzuh yayin yanke hukunci a Accra, babban birnin Ghana.


Tutar masu neman yantar da wani yanki na kasar Ghana hsgf/Nyakpo

Wanda ya kafa kungiyar Michael Koku Kwabla zai share tsawon shekaru biyar da tarar dalar Amurka 940 (kusan Yuro 860) a gidan yari, yayin da sauran mambobin kungiyar Nene Kwaku da Emmanuel Afedo da Abednego Mawena aka yanke musu hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari kowannen su.

A shekara ta 2017, aka kama shugabannin ‘yan aware a yammacin Togoland tare da hana su duk wani yukunri gudanar da ayukan su .

Yankin kogin Volta yana da kabilu da yawa kuma tarihinsa na baya-bayan nan ya samo asali ne daga turawan mulkin mallaka guda uku.

Wasu daga cikin mutanen yankunan da suke goyan bayan yantar da yankin Togoland
Wasu daga cikin mutanen yankunan da suke goyan bayan yantar da yankin Togoland hsgf/Nyakpo

Birtania ta mamaye mafi yawan abin da ya kunshi Ghana da Jamus da ke rike da kasar Togo a yanzu.

Bayan yakin duniya na farko da kuma shan kashi da Jamus ta yi, Birtania da Faransa sun raba kayan Jamusawa a tsakaninsu. Faransa ta dauki Togo a yau.

Biritania ta kwace Togoland na Biritaniya, yankin da aka hade cikin Ghana a 1956 bayan faduwar daular a Afirka.

‘Yan awaren dai sun ce yankin na da nasa tarihi da al’adu kuma suna son mayar da yankin ya zama kasa mai cin gashin kanta

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.