A yau asabar kotu ta sallami tsohon Firaministan Mali Moussa Mara ,wanda ya share shekara ɗaya a kurkuku.An kama shi,bayan da aka tuhume shi da furta kalaman da suka saɓawa dokokin majalisar soji da ke mulkin wannan ƙasa.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Moussa Mara ya riƙe mukamin Firaminista tsawon watanni takwas daga 2014 zuwa 2015,a ranar 1 ga watan Agusta na 2025,ne kotu ta zartas da hukunci ɗaure shi,hakan bai hana shi furta kalamai na cewa nan gaba ƴan ƙasar za su mori sauyi.
Wadanan kalamai na daga cikin ababen da suka janyowa tsohon Firaministan matsaloli da majalisar sojin wannan ƙasa.
Kotun ɗaukaka kara ta Bamako ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a watan Fabrairun 2026,bayan soke ɗaya, da kuma tarar CFA 500,000 (Euro 762). Wandan hakan ke dada tabbatar da hukuncin da kotu ta zartasa a shari’ar farko a ranar 27 ga Oktoba, 2025.
Wasu daga cikin masu goyawa tsohon Firaminsta Moussa Mara baya sun tabbatar da sallamar da aka yi masa,kamar yada wani daga jam’iyyar Yelema ya shaidawa kamfanin dillancin labaren Faransa na AFP cewa shugabansu na kan hanyarsa ta komawa gida daga gidan yari.
Wata majiya daga bangaren shari’a ta tabbatar da bayanin sakinsa ga AFP.
Crédit: Lien source