Majalisar Ghana ta fusata da matakin Nana Akufo Addo

Kakakin Majalisar Ghana ya ki amincewa da sahale nadin wasu sabbin ministoci bisa kafa hujja da cewa har sai shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya sanya hannu a dokar haramta auren jinsi da Majalisar ta kada kuri’ar amincewa da ita a watan jiya amma har zuwa yanzu shugaban ya gaza sanya hannu.

Wallafawa ranar:

Minti 1

Ana dai ganin shugaba Nana Akufo-Addo na jan kafa wajen rattaba hannu kan kudirin don mayar da shi doka ne sakamakon kakkausar sukar da kudirin ke fuskanta daga kungiyoyin kare hakkin dan adam musamman daga kasashen Turai.

Kafin wannan mataki na Majalisar dai, shugaba Addo ya ce yana jiran hukuncin kotun kolin kasar gabanin rattaba hannu kan dokar, bayan da masu fafutukar tabbatar da auren na jinsi suka daukaka kara kan matakin.

Wasu alkaluma da aka tattara na nuna cewa galibin al’ummar Ghana na goyon bayan haramta auren na jinsi da kuma tanadin hukunci mai tsauri kan wadanda aka samu da aikatawa ko kuma da goyon baya koma tallata shi.

Sai dai wasu bayanai na cewa, shugaba Akufo-Addo ya samu gargadi ne daga kasashen duniya da hukumomin bayar da lamuni da ke neman lallai kar ya sanya hannu a kudirin don mayar da shi dokar.

Ghana dai ba ita ce kasar farko da ke fuskantar matsala wajen aiwatar da wannan doka ta haramta auren jinsi ba, domin kuwa makamancin lamarin da ke faruwa a Kenya kenan, inda har zuwa yanzu kungiyoyin addinai ke ci gaba da gangami don kalubalantar mahukunta.

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.