Morocco,DRCongo da Ghana sun shafe akalla shekaru arba’in suna neman sake lashe kofin Afirka

Kasashen Morocco da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da Ghana sun shafe akalla shekaru arba’in suna sa ganin sun sake daga wannan kofin kwallon kafar Afirka.

Wallafawa ranar:

Minti 3

Yanzu haka,kowane daga cikin wadannan kungiyoyi na sa ran ganin a wannan gangami na 34 na gasar cin kofin Afrika  dake gudana  akasar ta Cote D’Ivoire  sun koma gida da wannan kofi.

 Kamar dai yada muka saba ,za um kawo na mu sharhi inda yanzu haka ga wasu tsofaffin zakarun Afirka suke ganin cewa an samu sauyi a fanin da ya shafi lankata da gogewa a fagen tamola.

Suna bayyana cewa babu karamar kungiya a fanin da ya sahfi kwallon kafa a wannan zamani.

Yayin da za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2024 a ranar 13 ga watan Janairu nan, galibin kasashe uku ne ke fatan ganin sun tsallake wannan yanayi na jira da suke cikin sa .

Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka don gasar 2015 © rfi

A bangaren da ya shafi kasar Maroko da farko, mafarkin samun nasara a gasar cin kofin kasashen Afrika na biyu yau da shekaru 48.

 Kungiyar ta Morocco da aka yiwa sunan Zakunan tsaunin Atlas ta dauki kofin sau daya ne kawai, a shekarar 1976 a kasar Habasha, inda aka tsayar da wanda ya yi nasara a gasar da aka yi a matsayin wasan karshe da aka buga tsakanin Morocco, Guinea, Nigeria da Masar.

Nasarar da ‘yan Morocco suka yi da Masar (2-1) da Najeriya (2-1) da kuma wasan da suka yi da Guinea (1-1) ya ba su damar lashe gasar cin kofin nahiyar ta farko a tarihinsu.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) Patrice Motsepe yayin gabatar da jawabi a taron fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 a filin wasa na Parc des Expositions da ke birnin Abidjan, ranar 12 ga Oktoba, 2023.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) Patrice Motsepe yayin gabatar da jawabi a taron fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 a filin wasa na Parc des Expositions da ke birnin Abidjan, ranar 12 ga Oktoba, 2023. © AFP

To sai dai  tun daga lokacin, tarihinsu na Afirka bai canza ba.

Kungiyar Atlas Lions dai ta sake buga wasan karshe ne a karawar da suka yi da Tunisia a shekarar 2004, inda suka sha kashi (1-2).

Da kamo hanya ta zuwa kasar Cote D’Ivoire  yan wasan ta Morocco sun bayyana cewa za je can don buga wasan kwallon kafa, da kuma komawa gida da wannan kofi a cewar  Walid Regragui mai horar da wannan kungiya.

Wasu daga cikin yan wasan Morocco da kocin kasar Walid Regragui zai yi dogaro da su sun hada da  Hakim Ziyech (Galatasaray), Achraf Hakimi (PSG), Sofyan Amrabat (Manchester United), Youssef En-Nesyri (Sevilla FC) da Yassine Bounou (Al-Hilal). Ya kuma kira matasa ‘yan wasa kamar Ismael Saibari (PSV Eindhoven) ko Chadi Riad (Real Betis).

Morocco za ta kara da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Zambia da Tanzaniya a rukunin F.

Tawagar Senegal kenan lokacin da ta dauki kofin nahiyar Afirka a kasar Kamaru
Tawagar Senegal kenan lokacin da ta dauki kofin nahiyar Afirka a kasar Kamaru © AFP

A karshe inda wannan kofin ya kubuce mata a Cote D’Ivoire,Morocco z ata karbi bakucin gasar gaba a 2025 a kasarta,mai yiyuwa mafarkin ta ya tabbata na dawo da kofin Afirka gida.

 Jamhuriyar Demokuraddiyar Congo da aka yiwa sunan  Damisa sau biyu ta lashe wannan kofi a gasar a shekarar 1968 a Habasha inda ta doke da 1-0 Ghana da kuma 1974 a Masar inda ta doke da 2-0  Zambia, tun daga lokacin les  Leopards  ko Damisa ta kasa yin nasara.

 Jadawalin kasashen da suka taba lashe wannan kofin Afirka.

• 1957: Masar

• 1959: Masar

• 1962: Habasha

• 1963: Ghana

• 1965: Ghana

• 1968: Congo

• 1970: Sudan

• 1972: Congo

• 1974: Congo-Zaire

• 1976: Morocco

• 1978: Ghana

• 1980: Najeriya

• 1982: Ghana

• 1984: Kamaru

• 1986: Masar

• 1988: Kamaru

• 1990: Algeria

• 1992: Cote D’Ivoire

• 1994: Najeriya

• 1996: Afirka ta Kudu

• 1998: Masar

• 2000: Kamaru

• 2002: Kamaru

• 2004: Tunisiya

• 2006: Masar

• 2008: Masar

• 2010: Masar

• 2012: Zambia

• 2013: Najeriya

• 2015: Cote D’Ivoire

• 2017: Kamaru

• 2019: Algeria

• 2021: Senegal

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.