Ƴan ci ranin da Amurka ta jibge a Congo na cikin mawuyacin hali

Baƙi ƴan ƙasashen waje da Amurka ta tura Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun bayyana damuwa kan halin da suke ciki a ƙasar mai fama da rikici. 

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Akasari waɗanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya zanta da su ƴan ƙasashen Latin Amurka ne, da suke ce ba haka suka zata ba, lokacin da suka nemi zaman mafaka a Amurka, amma sun tsinci kansu a wata ƙasar Afirka mai fama da rikici.

Gabirela ƴar asalin ƙasar Colombia mai shekaru 30, ta ce sun kwashe kusan sa’o’i 27 daga Amurka zuwa Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Demokradiyar Congo, cikin jirgin sama hannayensu da ƙafafunsu a ɗaure.

Demokradiyar Congo wadda ke ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka amince su karɓi ƴan ci-rani da aka kora daga Amurka, na cikin ƙasashe 15 mafi talauci a duniya, da kuma tsananin buƙatar jinƙai da yaƙi da mayaƙan M23 a gabashin ƙasar ya haddasa.

A watan Afrilu, rukunin farko na ƴan gudun hijirar suka isa ƙasar da ke tsakiyar Afirka, ƙarƙashin wani shirin gwamnatin shugaba Donald Trump mai cike da cece-kuce na korar ƴan ƙasashen waje marasa takardu zuwa wasu ƙasashen Afirka da suka shiga yarjejeniyar.

Sauran ƙasashe da suka amince da karɓar baƙin na Amurka sun haɗa da Kamaru da Equatorial Guinea da Eswatini da Ghana da Rwanda da kuma Sudan ta Kudu.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.