Burkina Faso da ta shafe kusan shekaru huɗu ƙarƙashin mulkin soji da Kyaftin Ibrahim Traore ke jagoranta, ta sanar da dakatar da babbar ƙungiyar ɗaliban ƙasar na tsawon watanni uku, kwanaki bayan tsare da wani babban malami da ake zargi da sukar gwamnati.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
A cikin wata sanarwa da gamayyar ƙungiyoyin Musulumi ta Burkina Faso FAIB ta fitar, ta ce a yammaci ranar Talata ne dai aka kama Imam Kindo,ba tareda sanar da dallilan da suka kai ga kama babban mallamin ba.
Iyalan shahararren malamin addinin Islama a Burkina Faso Mohamad Ishaq Kindo, sun ce jami’in ƴansanda sun kama shi a babban birnin ƙasar Ouagadougou, kwana biyu bayan sukar gwamnatin sojin ƙasar da ya yi.
Ƙungiyar ta ce tana bin dukkanin matakan da suka kamata, don ganin ta samu cikakken bayanan kamashi daga wajen hukumomi, da kuma samar da mafita akan lamarin.
Ko a tsakiyar watan Afrilu,hukumomin ƙasar sun tsare Mahmoud Barro wani mallami a garin Bobo Dioulasso,wanda ya furta kalamai da aka dangata da suka ga hukumomin sojin ƙasar.
Majalisar sojin ƙasar ba tsaya nan,ko a jiya laraba ta sanar da dakatar da ƙungiyar dalibai ta ƙasa wato UGEB,wanda yanzu haka shugabaninta ke tsare.
Ranar 19 ga watan Mayu ne shugabanin ƙungiyar ta UGEB suka yi suka tare da bayyana rashin jin dadin su da tsarin shugabanci duk da matakan da majalisar sojin ƙasar ta dauka wajen yaki da ta’addanci da kuma samarwa jama’a ababen more rayuwa.
Crédit: Lien source