Dakarun Mali sun ƙaddamar da hare-hare kan maɓuyar ƴan ta’adda a arewacin ƙasar

A Mali, rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da ƙaddamar da jerin hare-hare a kan ƴan ta’adda a tsakiya da kuma arewacin Bamako, dai-dai lokacin da tawagar manyan motocin dako suka isa babban birnin ƙasar.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Rundanar sojin Mali ce ta fitar da sanarwar da ke bayyana cewa dakarun ta sun yi ɓarin wuta kan ƴan ta’adda a yankunan Koulikouro da Mopti a ƙarshen makon da ya gabata.

Haka zalika, an jiyo ƙarin saukar bama-bamai da safiyar jiya Talata a birnin Kidal na arewaci, inda gidaje da dama suka rushe yayin da wani mazaunin yankin guda ya ɓace.

Ƴan tawayen Abzinawa da birnin na Kidal ne ƙarƙashin ikon su sun tabbatar da afkuwar harin, inda suka ce babu wanda ya rasa ransa, kodayake kawo yanzu ba a tabbatar da hakan ba daga sauran majiyoyi.

Duk da cewa rundunar sojin Mali ba ta sanar da harin na Kidal ba, amma dai ta ce ta kai yankin Koulikouro inda ta samu nasarar halaka ƴan ta’adda aƙalla 65, baya ga lalata wata maɓoyar ƴan ta’adda a kusa da Sofara da ke yankin Mopti.

A gefe guda, rundunar ta ce tawagar manyan tankoki 765 sun isa Bamako tare da rakiyar dakarun ƙasar, duk da haramcin shigar da kayayyaki da mayaƙan JNIM da ke da alaƙa da al-Qaeda suka ƙaƙaba a ƙasar ta yammacin Afrika.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.