Ebolar da Congo ke fuskanta ta kama hanyar zama mafi muni a tarihi- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana damuwa matuƙa da yadda annobar Ebola ke ci gaba da yaɗuwa a sassan Congo bayanda a yanzu haka ta fantsama yankuna 5 na ƙasar tare da kisan mutane dubu 1 da 587 daga cikin mutum dubu 3 da 605 da suka kamu da ita.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Cikin wasu bayanai da WHO ta fitar a jiya Asabar ta yi gargaɗin cewa matuƙar ba a ɗauki matakan da suka kamata ba, cutar ka iya yaɗuwar da ba a taɓa hasashe ba, tare da zama mafi muni da aka taɓa tani a tarihi.

Kalaman na WHO kai tsaye na matsayin gyara ga alƙaluman da ke nuna cewa annobar cutar ta Ebola a wannan karon ita ce ta biyu mafi muni da Congo ta taɓa fuskanta.

WHO ta ce akwai fargaba matuƙa kan yadda cutar ke saurin yaɗuwa tun bayan ɓullarta a ranar 15 ga watan Mayu inda kawo yanzu ta fantsama a a Larduna har 5 na jamhuriyyar Congo wadda ke matsayin mafi sauri da aka taɓa gani a tarihi.

A cewar WHO ƙoƙarin da mahukunta Congo suka yi na hana cutar bazuwa daga Mongbwalu na lardin Ituri ya ci tura inda cikin watanni 2 da suka gabata ta bijirewa dukkanin matakan da ake ɗauka.

Yanzu haka ana ganin yaɗuwar cutar ta Ebola a larduna irin Ituri da Arewacin Kivu kana Kudancin Kivu sai kuma Haut-Uélé da Tshopo, inda ta fantsama a cibiyoyin lafiya har 49.

Makon da muka yi bankwana da shi a cewar WHO cikin alƙaluman da ta fitar shi ne mafi yawan masu kamuwa da cutar tun bayan ɓullarta inda aka samu mutane 567 sabbin kamuwa da kuma mutane 296 da cutar ta kashe.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.