Fadar shugaban Jamhuriyar Benin a yau asabar ta sanar da yiwa ɗaya daga cikin ƴan adawa da ake tsare da shi afuwa. Kotu ta zartas da hukuncin ɗauri ga Julien Kandé Kansou, memba na babbar jam’iyyar adawa ta Benin, hukuncin ɗaurin shekaru biyu a watan Afrilu, musamman saboda « tunzura mutane ga tawaye.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Julien Kandé Kansou,ya sha’ara wajen rubuce-rubuce da wakokin na sukar gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Patrice Talon da gwamnatinsa.
A ƙarshen watan Afrilu, Kotun ta yanke masa hukunci bisa laifin « cin zarafi,ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta,baya ga haka an same shi da laifin tunzura mutane ga tawaye. » saboda rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.
Shugaban ƙasa Romuald Wadagni ya yafe masa ƴan lokuta bayan bikin zagayowar cika shekaru 66 da samun incin kai a yau asabar a birnin Kwatanu.
Ƴan adawa sun tabbatar da wamnnan sallama daga gidan yari,musaman daga bangaren Les Democrates.
Babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin ƙasar ta Benin.
Baya ga wannan ɗan adawa ,wasu daga cikin masu sukar gwamnatin da ta shude na tsare a gidan yari,wandada suka hada da Steve Amoussou, wanda ake zargi da kasancewa mai fafutukar kare haƙƙin jama’a ta yanar gizo, wanda ke sukar gwamnati a ƙarƙashin sunan « Brother Hounvi, » an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari.
Crédit: Lien source