‘Yan gudun hijirar Mali na neman ficewar sojojin Rasha daga ƙasarsu

Dubun-dubatar ‘yan gudun hijirar Mali da ke sansanin Mbera a Mauritania sun bayyana cewa, babban fatansu shi ne janyewar dakarun Rasha na Wagner domin su samu damar komawa ƙasarsu lafiya.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

‘Yan gudun hijirar suna zargin sojojin hayar da aikata kisan gilla, fyade, da azabtar da fararen hula a lokacin da suke gudanar da ayyukan yaƙi tare da dakarun gwamnatin sojin Mali.

A ƙarshen watan Afrilu ne, ƙungiyar ‘yan tawayen abzinawa da ke aikin haɗin gwiwa da mayaƙan JNIM suka ƙaddamar da wani babban hari, inda suka tilasta wa sojojin Rasha da na Mali tserewa daga manyan garuruwan arewacin ƙasar kamar Kidal, Tessalit, da Agelok.

Aƙalla ‘yan Mali 120,000 ne ke zaune a sansanin Mbera da ke cikin ƙasar Mauritania, kuma hukumomin agaji na fargabar cewa sabon rikicin zai iya janyo ƙarin kwararar mutane.

Mutane da dama a sansanonin na zargin gwamnatin mulkin sojan Mali da laifin janyo dakarun na Rasha, matakin da suka ce ya daɗa ruruta wutar rikici a maimakon kawo zaman lafiya.

Kakakin ‘yan tawayen Azawad, Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya bayyana ƙarara a yayin wata ziyara a Paris cewa babban burinsu shi ne korar dakarun Rasha gaba ɗaya daga ƙasar Mali.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.