DR Congo da M23 sun amince da tsagaita wuta da dawo da ayyukan jin ƙai

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da ƙungiyar ƴan tawayen M23 sun cimma matsaya kan yadda za a sauƙaƙa ayyukan jin ƙai da kai taimako ga mabuƙata da kuma sakin fursunoni cikin kwanaki 10.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

A cewar wata sanarwa mai ɗauke da kwanann watan 19 ga Afirilu da muke ciki, an cimma wannan matsaya bayan wata tattaunawa a Switzerland.

Tun shekarar 2021 ƙungiyar M23 da ke samun goyan bayan Rwanda ta ƙwace iko da gabashin Congo, yankin ya sha fama da rikici tsawon shekaru 30 da suka gabata.

Ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya wanda Amurka ke shiga tsakani a watan Disambar da ya gabata, sai dai faɗa ya ƙara ɓarkewa. Qatar dai ta ci gaba da jagoratar tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu daga ranar 13 zuwa 17 ga watan Afirulu da muke ciki.

A cewar sanarwar da masu shiga tsakani da kuma DR Congo da da M23 suka fitar, sun sanar da amincewa da muhimmincin da ke tattare da ayyukan jin ƙai, da kuma ceton rayukan jama’a a gabashin Congo, ɓangarorin sun yi alƙawarin tabbatar da ayyuka na jin kai ba tare da kawo cikas ba.

Harila yau sun amince da yin aiki da duk wasu dokokin duniya na ayyukan jin kai da kuma na kare haƙƙin ɗan adam da dokokin ƴan gudun hijira na duniya, sun kuma sha alwashin kaucewa aiwatar da duk wani abu da zai kawo tazgaro.

Baya ga haka ɓangarorin sun aminta da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 10 da kuma sanya hannu kan yarjejeniya don yin haɗin gwiwa wurin ganin an yi aiki da da yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin tsakaninsu.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.