Amurka za ta kwashe ƴan Afghanistan 1,100 da suka taimaka mata a yaƙi zuwa Congo

Gwamnatin shugaba Donald Trump na duba yiwuwar kwashe jami’an Afghanistan 1,100 da suka taimakawa dakarun Amurka lokacin yaƙinta da Kabul, zuwa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Tattaunawar da Amurka ta shiga da Congo don jigbe jami’an Afghanistan ɗin a cikin ƙasar na zuwa ne bayan matakin da Donald Trump ya ɗauka na katse wani shiri da ke bai wa Afghanistawan da suka taimakawa Washington a yaƙi damar dawowa zama a cikin ƙasar.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa Amurka ta kwashe waɗananan jami’ai fiye da 1000 zuwa Qatar don kare su saboda taimakon da suka bata lokacin yaƙinta da Afghanistan, gabanin komawar gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Taliban.

Cikin waɗannan jami’ai, akwai waɗanda suka taka rawa wajen bai wa Amurka bayanan sirri, da masu tafumta, da kuma wasu da ke da alaƙa da dakarun sojin Amurka, kuma tawagar jami’an ta ƙunshi yara fiye da 400.

Shugaban ƙungiyar AfganEvac, Shawn Vandiver da ya tabbatar da haka ya ce ya samu bayanai daga majiyoyi masu tushe cewar Afghanistawa 900  cikin dubu 1,100 sun samu damar komawa Amurka da zama, yayin da 200 da basu samu Washington za ta tsugunar dasu a Congo.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Kinshasha ke fuskantar matsanancin rikicin da ya raba fiye da mutane miliyan 8 da muhallansu a cewar alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.