A jiya juma’a ce ministan harkokin wajen Burkinabe ya yi Allah wadai da kalaman da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 30 ga Yuli, wanda ya danganta rashin tsaron da ke faruwa a arewacin Najeriya da sakaci da rashin bayar da kulawa da ta dace daga ƙasashen Sahel maƙwabta.
Wallafawa ranar:
Minti 2 Lokacin karatu
Ƙasashen kawancen Sahel na AES da suka hada da Nijar ,Mali,Burkina Faso ta bakin ministan harkokin wajen Burkina Faso sun bayyana rashin gamsuwar su biyo bayan kalaman shugaban na Najeriya,da babbar murya Karamoko Jean-Marie Traoré a jiya juma’a ya na mai bayyana irin jan kokarin da wadanan ƙasashe da suka hada da Nijar,Mali da Burkina Faso ke yi na ganin an kawo karshen ayukan ta’addanci,wanda wasu daga cikin masu fada a ji a Najeriya ke tallafawa ayukan ta’addanci, ministan ya bukaci Najeriya ta sake duba tsarin da take da shi a kai..
Kalaman na Ministan harkokin wajen Burkina Faso na zuwa ne bayan da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabanin gargajiya a ranar 30 ga watan yuli inda ya danganta wasu daga cikin matsaloli na tsaro da sace-sacen mutane a arewacin Najeriya ga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga ƙasashe maƙwabta.
Wannan ya sa Ministan harkokin waje na Burkina, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya fitar da wanan sanarwa mai ɗauke da sanya hannunsa.A cikin takardar, ya jaddada cewa ta’addanci barazana ce gama gari.
« Burkina Faso, Mali, Nijar, da Najeriya suna fuskantar makiyi ɗaya, » in ji ministan harkokin wajen ta Burkina Faso.Wakilan ƙasashe uku na AES, waɗanda suka yi taro a Ouagadougou, sun kira babban jami’in hulda da jama’a na Najeriya, suna yin Allah wadai da kalaman da Bola Ahmed Tinubu, waɗanda suka ɗauka a matsayin « ba daidai ba. » Ministan harkokin wajen Burkinabe ya tabbatar da cewa, ta hanyar kalamansa, shugaban Najeriya yana raina ƙoƙarin da sojojin AES suka yi wajen yaƙi da ta’addanci. « Ba mu da alhakin abin da ke faruwa da mu. Maƙiyan gaske suna wani wuri, » a cewar minstan na Burkina Faso.
A cikin ‘yan shekarun nan, tsaro ya tabarbare sosai a arewa maso yammacin Najeriya, tare da kan iyakarta da Nijar. Dangantaka tsakanin Abuja da maƙwabtanta ta riga ta yi tsami a shekarar 2023, bayan juyin mulkin da aka yi wa Mohamed Bazoum.
Crédit: Lien source