An soma shari’ar sojoji 84 da ake tuhuma da baro fagen daga da « ɓatar da harsasai » a DRCongo

A Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a yankin Kisangani, lardin Tshopo, ana shari’ar sojoji sama da 80 na rundunar sojin ƙasar da ake tuhuma da baro fagen daga da kuma ƙin yaƙi, » da « ɓatar da harsasai » a farkon wannan shekarar.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Rahotanni daga zauren na bayyana cewa,hakan ta faru ne a Pinga, a yankin Walikale na Arewacin Kivu,inda wasu sojoji suka bukaci karin albashi a dai dai lokacin da ake cikin yaki da ƴan tawayen M23 da ke samun goyan bayan Rwanda.

An soma shari’ar ne a ranar Laraba, 29 ga Afrilu, a kotun soji ta Kisangani. Akala sojoji 84 ne suka bayyana gaban alkalin kotun soji bayan samun su daga cikin masu laifi.

A cewar ofishin mai gabatar da ƙara na ƙasar, abubuwan sun faru ne tun daga watan Fabrairu a garin Pinga lokacin da waɗannan sojoji suka ƙi yaƙi,lamarin da ya haifar da harbe-harbe a garin. Irin wannan zanga-zangar gama gari haramun ne a cikin rundunar sojoji.

Kwamandan yankin na Uku ne ya gabatar da karar a kotu, yana fatan shari’ar za ta kawo sauyi da nufin sake dawo da martabar soji a wanan ƙasa da aka share dogon lokaci ana fama da rashi tsaro musaman a yankin Kivu.

Wani lauya mai kare wadanda ake tuhuma ya nuna rashin shaidar kuma tun daga farko ya ce « wannan shari’ar tana kawo cikas ga rundunar. » Waɗannan sojojin, waɗanda aka tsare na tsawon watanni biyu a gidan yarin soja na Kisangani, suna fuskantar ɗaurin rai da rai.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.