Birnin Sake da ke Gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo na ci gaba da kasancewa cikin tashin hankali da fargaba sakamakon rikicin dake faruwa tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen M23.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Birnin ya kasance wata babbar cibya mai mahimmanci wajen kare birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
A farkon shekarar 2026, an bayar da rahoton cewa dakarun M23 sun ƙaddamar da gagarumin hari a garin Sake da nufin kakkaɓe dakarun gwamnati domin samun hanyar kutsa kai zuwa Goma.
Rahotanni daga ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun nuna cewa ‘yan tawayen M23 sun tilastawa dubban mutane barin gidajensu a garin Sake, inda aka kora su zuwa birnin Goma.
Baya ga sojojin gwamnati, akwai dakarun sa-kai da ake kira Wazalendu masu kishin ƙasa waɗanda ke faɗa da ‘yan tawayen M23.
Waɗannan ƙungiyoyi suma ana zargin su da tafka wasu ayyukan cin zarafin fararen hula a sassan lardin Kivu ta Kudu.
Duk da cewa an ƙulla yarjejeniyoyin tsagaita wuta a kasashen Qatar da Amurka, faɗan ya ci gaba da ƙazanta tare da amfani da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuki kan fararen hula.
Rikicin ya tilastawa miliyoyin mutane barin muhallansu a sassan gabashin Congo, inda mutane da dama ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira cikin mawuyacin hali.
Crédit: Lien source