HRW ta zargi sojin hayar Rasha da kashe fararen hula a Mali

Ƙungiyar Human Rights Watch ta ce sojin haya na Rasha sun kashe fararen hula takwas ciki har da yara uku a wani hari ta sama da suka kai a ƙasar Mali a watan da ya gabata. Ƙungiyar ta ce wannan harin kai tsaye ya shafi fararen hula ba tare da ware wadanda ake rikici da su ba.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Africa Corps, wadda Ma’aikatar Tsaron Rasha ta kafa, ta karɓi yawancin ayyukan tsohuwar rundunar sojin haya ta Wagner Group a nahiyar Afirka.

Rundunar na taimaka wa gwamnatin mulkin sojin Mali wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Binciken da Human Rights Watch ta gudanar ya nuna cewa wani jirgin yaƙi kirar Sukhoi Su-24, wanda wasu jami’an sojin Mali biyu suka tabbatar da nau’insa, ya jefa aƙalla bama-bamai biyu a ƙauyen Kyrnia da ke yankin Mopti a tsakiyar Mali a ranar 15 ga Yuni.

Rahoton ya ce bam na farko ya faɗa kusa da gidan dagacin ƙauyen, inda ya kashe matarsa da ‘ya’yansa biyu tare da wani yaro, yayinda Bam na biyu kuma ya faɗa kasuwar shanu da ke kusa, inda ya kashe maza huɗu.

Human Rights Watch ta ƙara da cewa babu wata shaida da ke nuna cewa an kashe mayaƙan ƙungiyar (JNIM) mai alaƙa da Al-Qaeeda, wadda rahoton ya ce ta shafe kusan shekaru shida tana iko da ƙauyen.

A nata ɓangaren, rundunar Africa Corps ta wallafa bidiyon harin daga sama a shafukanta na Facebook da X, inda ta ce ta kai hari a ranar 15 ga Yuni kan wani wurin taruwar ƙungiyoyin da ta kira ‘yan ta’adda a yankin Mopti.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.