Hukumomin Burkina Faso sun rufe wani babban masallacin da ke Ouagadougou

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso karkashin shugabancin Kyaftin Ibrahim Traore ta yanke shawarar rufe babban masallacin Sunni da ke Ouagadougou,da nufin gujewa tarzoma da kan iya biyo bayan tsare wasu daga cikin magabata.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

 

A yan kwanaki da suka gabata an fuskanci suka daga wasu mutane kan abida suka kira rashin shugabanci na gari,al’amarin da ya kai ga kama limamin mabiya Sunni kuma mai wa’azi, Mohamad Ishaq Kindo a ranar Talata.

Burkina Faso na daga cikin ƙasashen da ake da musulmai da kusan kashi 60% na al’ummarta,sanarwar mai dauke da sanya hannun gwamnan babban birnin ƙasar Abdoulaye Bassinga,na zuwa a wani lokaci da hukumomin soji suka haramta duk wata zanga-zanga a ƙasar.

A baya,limamin da aka kama ya yi Allah wadai da wata doka da hukumomin sojin suka aiwatar ,wacce ke kuma takaita amfani da ‘yancin addini.

Rufe masallacin da ke tsakiyar babban birnin Ouagadougou,na zuwa ne bayan da jama’a suka soma taruwa a wurin da nufin ganin an sako limamin,a maimakon wurin ibada,ya kama hanayr zama wani dandali na taruwa,wanda ya kai jami’an tsaro ga tarwatsa jama’a.

Ƴansanda na tsare da mutane da dama da aka kama a harabar masallaci.

Ƴansanda na tasre da kusan mutane 100 daga cikin magoya bayan limamin a cewar wata majiyar tsaro,mutanen da aka garzaya da su zuwa sansanin horar da ƴansanda na CRS.

A cikin bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta,ana iya ganin kimanin maza ɗari sanye da kayan soja suna addu’a yayin da sojoji ke yi musu ba’a.

A wasu bidiyon, ana iya ganin wasu daga cikin waɗannan mutanen ana dukansu ko kuma suna yin atisayen soja.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.