Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kife a mahadar kogunan Kasai da Sankuru

A tsakiyar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ana ci gaba da bincike bayan da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife a mahadar kogunan Kasai da Sankuru a yankin Ilebo. Adadin wadanda suka mutu na wucin gadi da hukumomi suka fitar a ranar Juma’a, ya kai akalla 20, 80 suka tsira,sama da mutane 100 da har yanzu babu duriyar su.

Wallafawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Ana ci gaba da bincike da sa ran ko za a samu wasu da rai bayan wannan haɗari,inda ake kyautata zaton hakan a cewar wani jami’in Red Cross a yankin.

Kungiyoyin ceto sun ci gaba da bincike a bakin kogin a jiya Asabar,suna neman wadanda suka tsira ko kuma gawarwwaki.

A cewar mai kula da yankin Ilebo, François Kabula, sama da mutane 200 ne ke cikin jirgin ruwan, wanda ke tafiya daga tashar jiragen ruwa ta Kalina zuwa Ilebo, a lardin Sankuru. Daga cikin fasinjojin akwai dalibai da yawa da suka dawo gida bayan jarrabawar karshen shekara.

A cewar wasu majiyoyi na gida jirgin ya bar tashar jiragen ruwa da daddare don guje wa binciken tsaro, duk da cewa ya cika da fasinjoji da kaya.

A mahadar kogunan Kasai da Sankuru, kwale-kwalen ya fashe kafin ya nutse. An ceto mutane 80 a cewar masunta da ke kusa.

Wannan na ɗaya daga cikin bala’i mafi muni da aka fuskanta a wannan shekara.Da jimawa ne aka yi ta kokawa kan rashin inganci sufurin jiragen ruwa masu ɗauko fasinjoji a wannan ƙasa.

Ƙungiyoyin farar hula a Ilebo sun yi Allah wadai da neman riba a kan lafiyar fasinjoji kuma suna neman a sanya takunkumi a kan masu jiragen ruwa, a tsaurara matakan tsaro ko da daddare, da kuma rigunan ceto na tilas.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.