Mali ta yi watsi da iƙirarin gwamnatin Amurka na ƙoƙarin shiga tsakani a yaƙin da ƙasar ta yankin Sahel ke yi da ƴan ta’addan JNIM mai biyayya ga ƙungiyar al’Qaeda da a baya-bayan nan suka zafafa hare-hare a ƙasar musamman bayan ƙawancensu da ƴan tawayen Abzinawa.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
A jawabinsa gaban taron manema labarai da ya gudana a birnin Bamako, ministan wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce babu gaskiya kan batun na yiwuwar kai harin Amurka a cikin ƙasar wanda ke matsayin martani ga rahoton Washington Post da ke cewa Donald Trump na duba yiwuwar kai hari kan ƴan ta’addan ƙasar.
A Larabar da ta gabata ne, rahotanni kan yiwuwar kai harin na Amurka a Mali ya karaɗe kafafen yaɗa labarai batun da Diop ke cewa babu wata tattaunawa tsakaninsu da Amurka kan hakan, hasalima kamar kowa suma sun tsinci labarin ne kafafen yaɗa labarai.
JNIM mai biyayya ga Al-Qaeda da ke aiwatar da harkokinta na ta’addanci a tsakan-kanin ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, jagoran ƙungiyar wato Ag Ghali na sahun waɗanda Amurka ta sanya a jerin ƴan ta’adda.
Abdoulaye Diop cikin jawabin nasa, ya ce Mali ba zata zuba ido har sai wata ƙasa ta zo ta magance mata matsalolin tsaron da ke damunta ba, ita da kanta za ta magance matsalolinta.
A cewar ministan basu da tabbacin batun kai harin daga gwamnatin Amurka ya fito domin kuwa ba a tuntuɓesu gabanin sanarwar ba.
Crédit: Lien source