Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf, ya fara gagarumar ziyarar aiki ta kwanaki biyu a birnin Bamako fadar gwamnatin Mali, wadda ya faro a ranar 12 ga watan Yuli, da ke matsayin ziyara irinta ta farko da wani babban jami’in ƙungiyar ya kai ƙasar ta yankin Sahel.
Wallafawa ranar:
Minti 1 Lokacin karatu
Tun a watan Yunin shekarar 2021, ƙungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali daga dukkan harkokinta biyo bayan juyin mulkin soji da ya faru a kasar.
Ziyarar ta Mahmoud Ali Youssouf na nuna sabon babi na nuna sha’awar AU wajen tafiya tare da Mali maimakon ci gaba da nuna mata ƙyama ta fannin diflomasiyya.
A yayin zaman nasa a Bamako, shugaban na AU ya gana da Shugaban mulkin rikon ƙwarya na ƙasar, Janar Assimi Goïta, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar kasar ta yankin sahel.
Babban abin da ya mamaye tattaunawar shi ne yadda za a ɓullowa matsalar tsaro da ta addabi yankin Sahel da kuma hanyoyin da ƙasar Mali za ta bi wajen komawa ga turbar dimokraɗiyya.
Tattaunawar ta gudana cikin yanayi na girmama juna da amincewa da kalubalen da ke gaban kasar.
Baya ga tarukan gwamnati, babban jami’in na AU ya kuma ziyarci ofisoshin rundunar wanzar da zaman lafiya da sasanta rikici ta kungiyar Tarayyar Afirka a Mali da shiyyar Sahel MISAHEL da ke Bamako.
Masana harkokin diflomasiyya na kallon wannan ziyara a matsayin wani babban mataki na samun sauki ga tsauraran matakan da aka kakaba wa Mali a baya.
Ana sa ran sakamakon wannan tattaunawa zai taimaka wajen sassauta takunkumi tare da samar da sabuwar dabarar hadin gwiwa tsakanin Tarayyar Afirka da kasashen da ke kawancen Sahel AES, abin da ake ganin zai taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yammacin Afirka.
Crédit: Lien source