Tedros Adhanom Ghebreyesus zai gana da Félix Tshisekedi a Kinshasa

Shugaban Hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya isa Jamhuriyar demokuradiyyar Congo a daren jiya Alhamis,ƙasar da annobar Ebola ta yi kamari,zai kuma ziyarci wasu daga cikin yankuna da jama’a ke fama da ebola a gobe asabar.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 2 Lokacin karatu

Rahotanni daga hukumar lafiya na bayyana cewa,an dage tafiyarsa zuwa Ituri,yanki da cutar Ebola ta bulla karo na 17 a ƙasar, wanda aka tsara tun farko a jiya Juma’a, har gobe Asabar.

Majiya na tabbatar da ganawa tsakanin Tedros da shugaban Congo Félix Tshisekedi a yau Juma’a.


Wasu daga cikin mutanen da Ebola ta kashe © REUTERS – Gradel Muyisa Mumbere摄影

Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo,na daga cikin jerin ƙasashen masu fama da talauci a duniya,aka kuma gano cutar ebola da ta sake bulla a ranar 15 ga Mayu a wasu yankuna na ƙasar mai yawan mutane da kusan milyan 100. Tun bayan samun labarin mutuwar marasa lafiya da suka kamu da ebola ne hukumar lafiya ta duniya da sauren ƙungiyoyi suka dau matakai na kira da kuma gargadi ga jama’a na aiki da umurnin likitoci.

Cutar ta ebola wadda ta riga ta kasance a larduna uku da kuma makwabciyar Uganda, inda aka samu mutane bakwai da suka kamu da cutar, aka kuma samu mutuwar mutane a wasu yankuna.

A Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, an samu mutuwar mutane 246 daga cikin wadanda ake zargi da kamuwa da cutar sama da 1,000.

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano maganin da ya dace a yi amfani da shi wajen murkushe wannan anoba,

Hukumar lafiya na ci gaba da gudanar da gwaje-gwaje a kan marar sa lafiya da burin ganin an kawo karshen ta cikin sauri kafin ta bazu zuwa wasu yankuna gida da wajen ƙasar.

Cutar Ebola, wacce ta kashe mutane sama da 15,000 a Afirka a cikin shekaru 50 da suka gabata, tana haifar da zazzabin jini mai tsanani da kuma saurin yaduwa.

Uganda da Rwanda kwanan nan sun rufe iyakokinsu da DRCongo.

A ranar laraba da ta gabata ne, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa Amurka ba za ta bar « kowane mutum ɗaya da ya kamu da cutar Ebola ya shiga » ƙasar ba.

Hukumar lafiya ta duniya bayan bayyana damuwa biyo bayan yaɗuwar cutar ta Ebola, ta bayyana cewa cutar na da haɗarin gaske ga lafiyar jama’ar DRCongo,zuwa mafi girman matakinta a makon da ya gabata.

Hukumar ta bayyana haɗarin ga sauran ƙasashe na yankin a matsayin « mai girma » amma har yanzu yana « ƙasa » a matakin duniya.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.