Zambia ta bi sahun Ghana wajen janyewa daga shirin tallafin lafiyar Amurka

Gwamnatin Zambia ta ce ba za ta amince da shirin taimakon kuɗaɗen tallafin lafiyar Amurka ba, wanda aka masa dabaibayi da wasu shariɗodin da suka kunshi ba su damar kai hannu a kan ma’adinan ƙasar ma su ɗimbin daraja.

Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:




Minti 1 Lokacin karatu

Ministan harkokin wajen Zambia Mulambo Haimbe ne ya fasa wannan kwai, in da ya ke cewa Amurkar ta musu tayin dala biliyan biyu a matsayin tallafin kula da harkokin lafiya nan da shekaru biyar ma su zuwa, ya yin da Zambia kuma za ta bata bayanan sirrin mutanen ƙasar ta.

Ministan ya kuma ce wani babban abin damuwa shi ne yadda Amurka ta gindaya yarjejeniyar kai wa ga ma’adinan Zambia a matsayin ɗaya daga cikin shariɗoɗin bada tallafin kuɗaɗen.

Ita dai gwamnatin Zambia ta bayyana cewar waɗannan yarjeniyoyi guda biyu ba su da alaƙa da juna, saboda haka babu dalilin gwamutsasu a wuri guda da kuma sanya su cikin shirin tallafin kuɗaɗen lafiyar.

Ita dai gwamnatin Amurka ta ce bata bayyanin yarjejeniyar da take ƙulla wa da ƙasashen duniya.

Rahotanni sun ce ƙasashen Afirka da dama sun rattaɓa hannu a kan irin wannan yarjejeniya da Amurka, sai dai ƙasashen Ghana da Zimbabwe da su ka yi watsi da ita.

Ministan na Zambia ya bayyana matsayin ƙasar sa ne sakamakon sukar da jakadan Amurka mai barin gado Michael Gonzales ya yi, wanda ya zargi ƙasar da ƙin amincewa da buƙatar karɓar tallafin kuɗaɗen, abinda Haimbe ya ki amincewa da shi.

Crédit: Lien source

Laisser un commentaire

Votre adresse email ne sera pas publiée.