A Brussels,wasu ƴan ƙasashen Mali,Nijar da Burkina Faso sun ƙaddamar da sabon ƙawance na dawo da demokuradiyya a yankin Sahel a hukumance a jiya, Asabar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Minti 2 Lokacin karatu
Ƙungiyar mai suna ADS,Alliance of Democrats of the Sahel (ADS),manufar ta a cewar wandada suka samar da ƙungiyar shina na kira da a dawo da tsarin mulki a ƙasashen Sahel karkashin ƙungiyar AES da suka hada da Nijar,Mali da Burkina Faso.
Ƙungiyar ADS wacce ke ikirarin ganin an dawo da tsarin demokuradiyya a yankin,ta nisanta kan ta daga ikirarin da ake na cewa kungiyar na da wata manufa daban.
wasu na mai bayyanyi iƙirarin bayar da ra’ayi daban-daban game da rikicin Sahelian kuma ta musanta cewa ita ‘yar adawa ce da ba ta da alaƙa da ainihin abubuwan da ke faruwa a yankin.
Dokta Marya Djibrine, shugabar wannan ƙungiya ta ADS,ta amsa cewa lalle manufar daya da masu adawa da wadanan sojoji,to sai dai ba su gwagwarmaya da suna wata jam’iyya ko wani gugun mutane,ta zargi gwamnatocin sojojin yanƙin Sahel da suka hada da Nijar,Mali da Burkina Faso da yin watsi da dimokuraɗiyya don ba da hujjar ci gaba da riƙe madafun iko.
A karshe Dokta Marya ta shelanta cewa,wadanan sojoji na ci gaba da rurruta cewa duk matsalolinsu sun samo asali ne daga dimokuraɗiyya.
Wannan sabuwar ƙungiya ta ADS a wannan bikin ƙadamar da ita,ta tabbatar da cewa akwai jan aiki nan gaba har idan ana son a cimma wannan maufa da dawo da dimokuradiyya a yankin na Sahel,don nuna wa mutane cewa ci gaba ba ya buƙatar kama-karya, sabili da haka mutane ba sa buƙatar a gaya musu abin da za su yi ko kokarin canza musu tunani.
Dokta Marya ta na mai kira ga jama’a na cewa ya dace mutane su kawar da wanan tunanin na cewa su ƙungiyar ‘yan gudun hijira ce da aka haifa nesa da Sahel.
Akwai ‘yan gudun hijira a cikinmu, amma waɗannan mutane ne da suka taru don su ce lokaci ya yi da za a yi aiki domin, idan ka ga yadda lamarin ke canzawa, ba za ka iya daina damuwa ba.
An kafa ƙungiyar Alliance of Sahel Democrats (ADS) a farkon watan Afrilu a Brussels ta hannun ‘yan adawa da aka kora daga ƙasashe uku na ƙungiyar AES da suka hada da Mali, Nijar, da Burkina Faso.
Sabuwar ƙungiyar ADS ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga cikin lumana don hambarar da gwamnatocin soji na ƙungiyar AES, waɗanda suka hau mulki ta hanyar juyin mulki kuma suka ci gaba da mulki ba tare da zaɓe ba.
Crédit: Lien source